Littafi Mai Tsarki

Zab 55:7-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. In tafi can nesa,In yi wurin zamana a hamada.

8. Zan hanzarta in nemi mafakaDaga iska mai ƙarfi da hadiri.”

9. Ka hallaka su, ya Ubangiji, ka birkitar da maganarsu,Gama na ga hargitsi da tawaye a birni.

10. Dare da rana suna ta yawo a kan garu suna ta kewaye birnin,Birnin kuwa cike yake da laifi da wahala.

11. Akwai hallaka a ko'ina,Tituna suna cike da azzalumai da 'yan danfara.

12. Da a ce maƙiyina ne yake mini ba'a,Da sai in jure.Da a ce abokin gābana ne yake shugabancina,Da sai in ɓuya masa.

13. Amma kai ne, aminina,Abokin aikina ne, abokina ne kuma!

14. Dā mukan yi taɗi da juna ƙwarai,Mukan tafi Haikali tare da sauran jama'a.