Littafi Mai Tsarki

Zab 52:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Me ya sa kake fariya da muguntarka,Ya kai, babban mutum?Ƙaunar Allah tana nan a koyaushe.

2. Kana shirya maƙarƙashiya don ka lalatar da waɗansu,Harshenka kamar aska mai kaifi yake.Kana ƙirƙiro ƙarairayi kullum.

3. Kana ƙaunar mugunta fiye da nagarta,Kana kuwa ƙaunar faɗar ƙarya fiye da gaskiya.

4. Kana jin daɗin cutar mutane da maganganunka,Ya kai, maƙaryaci!

5. Don haka Allah zai ɓata ka har abada,Zai kama ka, yă jawo ka daga alfarwarka,Zai kawar da kai daga ƙasar masu rai.

6. Adalai za su ga wannan, su ji tsoro,Za su yi maka dariya, su ce,

7. “Duba, ga mutumin da bai dogara ga AllahDon ya sami zaman lafiyarsa ba.A maimakon haka, sai ya dogara ga wadatarsa.Yana neman zaman lafiyarsa ta wurin muguntarsa.”

8. Amma ni, kamar itacen zaitun nake, wanda yake girma kusa da Haikalin Allah,Ina dogara ga madawwamiyar ƙaunarsa har abada abadin.

9. Zan gode maka, ya Ubangiji,Saboda abin da ka aikata.Zan dogara gare ka,Sa'ad da nake sujada tare da jama'arka,Domin kai mai alheri ne.