Littafi Mai Tsarki

Zab 51:16-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Ba ka son sadakoki, ai, da na ba ka,Ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa.

17. Hadayata, ita ce halin ladabi, ya Allah,Zuciya mai ladabi da biyayya,Ba za ka ƙi ba, ya Allah.

18. Ya Allah, ka yi wa Sihiyona alheri, ka taimake ta,Ka sāke gina garun Urushalima.

19. Sa'an nan za ka ji daɗin hadaya ta ainihi,Da dukan hadayun ƙonawa.Za a miƙa bijimai hadayu a bisa bagadenka.