Littafi Mai Tsarki

Zab 49:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku ji wannan, ko wannenku,Ku saurara jama'a duka na ko'ina,

2. Da manya da ƙanana duka ɗaya,Da attajirai da matalauta baki ɗaya.

3. Zan yi magana da hikima,Zan yi tunani mai ma'ana.