Littafi Mai Tsarki

Zab 49:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku ji wannan, ko wannenku,Ku saurara jama'a duka na ko'ina,

2. Da manya da ƙanana duka ɗaya,Da attajirai da matalauta baki ɗaya.

3. Zan yi magana da hikima,Zan yi tunani mai ma'ana.

4. Zan mai da hankalina ga ka-cici-ka-cici,In bayyana ma'anarsa sa'ad da nake kaɗa molo.

5. Don me zan ji tsoro a lokacin hatsari,Sa'ad da mugaye suka kewaye ni,

6. Mutanen da suke dogara ga dukiyarsu,Waɗanda suke fariya saboda yawan wadatarsu?

7. Har abada mutum ba zai iya fansar wani ba,Ba kuwa zai iya biyan kuɗin ransa ga Allah ba.

8. Gama kuɗin biyan ran mutum ba shi da iyaka.Abin da zai iya biya, sam ba zai isa ba,

9. Ba kuwa zai rayar da shi,Ko ya hana shi mutuwa har abada ba.

10. Yakan sa masu hikima su ma su mutu,Haka nan ma wawaye da mutanen banza,Za su mutu su bar dukiyarsu ga zuriyarsu.

11. Kaburburansu za su zama gidajensu har abada,Can za su kasance kullum,Ko da yake a dā suna da ƙasa ta kansu.

12. Girman mutum ba zai hana shi mutuwa ba,Zai mutu kamar dabba.

13. Dubi abin da zai faru ga waɗanda suke dogara ga kansu,Da irin ƙaddarar waɗanda dukiya ta ishe su.