Littafi Mai Tsarki

Zab 44:5-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Da ikonka muka kori abokan gābanmu,Saboda kasancewarka tare da muMuka rinjayi magabtanmu.

6. Ban dogara ga bakana ba,Takobina kuwa ba zai cece ni ba.

7. Amma ka cece mu daga abokan gābanmu,Ka kori waɗanda suke ƙinmu.

8. Za mu yabe ka kullum,Mu yi maka godiya har abada.”

9. Amma yanzu, ya Allah, ka yashe mu,Ka bari aka kore mu,Ba ka ƙara fita ka yi tafiya tare da sojojinmu ba.

10. Ka sa muka gudu daga gaban abokan gābanmu,Suka ƙwace abin da muke da shi.

11. Ka bari aka yanyanka mu kamar tumaki,Ka warwatsar da mu a baƙuwar ƙasa.

12. Ka sayar da jama'arkaA bakin 'yan kuɗi ƙalilan,Ba ka ci ribar cinikin ba.

13. Maƙwabtanmu suna yi mana dariya saboda kai,Suna yi mana ba'a, sun maishe mu abin wasa.

14. Ka maishe mu abin raini a wurin arna,Suna kaɗa mana kai, suna raina mu.

15. Kullum a cikin kunya nake,Kunya ta lulluɓe ni ɗungum,

16. Saboda dukan wulakanci,Da zagin da nake sha daga maƙiyana da abokan gābana.

17. Dukan wannan ya same mu,Ko da yake ba mu manta da kai ba,Ba mu kuma ta da alkawarin da ka yi da mu ba.