Littafi Mai Tsarki

Zab 44:15-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Kullum a cikin kunya nake,Kunya ta lulluɓe ni ɗungum,

16. Saboda dukan wulakanci,Da zagin da nake sha daga maƙiyana da abokan gābana.

17. Dukan wannan ya same mu,Ko da yake ba mu manta da kai ba,Ba mu kuma ta da alkawarin da ka yi da mu ba.

18. Ba mu ci amanarka ba,Ba mu ƙi yin biyayya da umarnanka ba.