Littafi Mai Tsarki

Zab 44:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da kunnuwanmu muka ji, ya Allah,Kakanninmu suka faɗa mana,Manya manyan abubuwa da ka aikata a lokacinsu,A zamanin dā,

2. Yadda kai da kanka ka kori arna,Ka dasa jama'arka a ƙasarsu,Yadda ka hori sauran al'umma,Amma ka sa jama'arka su wadata.

3. Ba da takubansu suka ci ƙasar ba,Ba kuwa da ikonsu suka rinjayi ƙasar ba,Amma da ikonka ne da kuma ƙarfinka,Ta wurin tabbatar musu kana tare da su,Kana nuna musu kana ƙaunarsu.

4. “Ya Allah, kai ne Sarkina,Ka ba jama'arka nasara.

5. Da ikonka muka kori abokan gābanmu,Saboda kasancewarka tare da muMuka rinjayi magabtanmu.

6. Ban dogara ga bakana ba,Takobina kuwa ba zai cece ni ba.

7. Amma ka cece mu daga abokan gābanmu,Ka kori waɗanda suke ƙinmu.

8. Za mu yabe ka kullum,Mu yi maka godiya har abada.”

9. Amma yanzu, ya Allah, ka yashe mu,Ka bari aka kore mu,Ba ka ƙara fita ka yi tafiya tare da sojojinmu ba.