Littafi Mai Tsarki

Zab 37:30-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Kalmomin mutumin kirki suna da hikima,Yana faɗar abin da yake daidai.

31. Yakan riƙe dokar Allahnsa a zuciyarsa, Ba ya kauce mata, faufau.

32. Mugu yakan yi fakon mutumin kirki,Yă yi ƙoƙari yă kashe shi,

33. Amma Ubangiji ba zai bar shi a hannun magabtansa ba,Ko kuwa yă bari a kāshe shiSa'ad da ake masa shari'a.

34. Ka sa zuciyarka ga UbangijiKa kiyaye dokokinsa,Shi zai ba ka ƙarfin da za ka mallaki ƙasar,Za ka kuwa ga an kori mugaye.

35. Na ga wani mugu, azzalumi,Ya fi kowa tsayi,Kamar itacen al'ul na Lebanon,

36. Amma bayan ƙanƙanen lokaci,Da na zaga, ban gan shi ba,Na neme shi, amma ban same shi ba.

37. Dubi mutumin kirki, ka lura da adali,Mutumin salama yakan sami zuriya,

38. Amma za a hallaka masu zunubi ƙaƙaf,Za a kuma shafe zuriyarsu.

39. Ubangiji yakan ceci adalai,Ya kiyaye su a lokatan wahala.

40. Yakan taimake su, yă kuɓutar da su,Yakan cece su daga mugaye,Gama sukan zo wurinsa don yă kāre su.