Littafi Mai Tsarki

Zab 37:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Kada ka damu saboda mugaye,Kada ka yi ƙyashin masu aikata abin da ba daidai ba.

2. Za su shuɗe kamar busasshiyar ciyawa,Za su mutu kamar yadda tsire-tsire suke bushewa.

3. Ka dogara ga Ubangiji ka aikata nagarta,Ka zauna a ƙasar, ka sami lafiya.

4. Ka nemi farin cikinka a wurin Ubangiji,Zai kuwa biya maka bukatarka.

5. Ka miƙa kanka ga Ubangiji,Ka dogara gare shi, zai kuwa taimake ka.

6. Zai sa nagartarka ta haskaka kamar haske,Adalcinka kuma yă haskaka kamar tsakar rana.

7. Ka natsu a gaban Ubangiji,Ka yi haƙuri, ka jira shi,Kada ka damu da waɗanda suke da dukiya,Ko su da suka yi nasara da aikata mugayen shirye-shiryensu.

8. Kada ka yi fushi, kada ka hasala!Kada ka damu! Gama ba zai yi maka amfanin kome ba.

9. Waɗanda suka dogara ga Ubangiji,Za su yi zamansu lafiya a ƙasar,Amma za a kori mugaye.

10. A ɗan ƙanƙanen lokaci mugaye za su shuɗe,Za ka neme su, amma ba za a same su ba,