Littafi Mai Tsarki

Zab 34:13-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. To, ku yi nisa da mugun baki,Da faɗar ƙarairayi.

14. Ku rabu da mugunta, ku aikata alheri,Ku yi marmarin salama, ku yi ƙoƙarin samunta.

15. Ubangiji yana lura da adalai,Yana kasa kunne ga koke-kokensu,

16. Amma yana ƙin masu aikata mugunta,Saboda haka har mutanensu sukan manta da su.

17. Adalai sukan yi kira ga Ubangiji, yakan kuwa kasa kunne,Yakan cece su daga dukan wahalarsu.

18. Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai,Yakan ceci waɗanda suka fid da zuciya.

19. Mutumin kirki yakan sha wahala da yawa,Amma Ubangiji yakan cece shi daga cikinsu duka.

20. Ubangiji yakan kiyaye shi sosai,Ba ko ɗaya daga cikin ƙasusuwansa da zai karye ba.

21. Mugunta za ta kashe mugu,Waɗanda suke ƙin adalai za a hukunta su.

22. Ubangiji zai fanshi bayinsa,Waɗanda suka tafi wurinsa neman mafakaZa a bar su da rai.