Littafi Mai Tsarki

Zab 33:9-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Da magana ya halicci duniya,Ta wurin umarninsa kowane abu ya bayyana.

10. Ubangiji yakan sassoke manufofin sauran al'umma,Yakan hana su aikata shirye-shiryensu.

11. Amma shirye-shiryensa sukan tabbata har abada.Nufe-nufensa kuma dawwamammu ne har abada.

12. Mai farin ciki ce al'ummar da Ubangiji yake Allahnta,Masu farin ciki ne jama'ar da Ubangiji ya zaɓo wa kansa!

13. Daga Sama Ubangiji ya dubo dukan 'yan adam.

14. Daga inda yake mulki, yakan dubo dukan mazaunan duniya.

15. Shi ya siffata tunaninsu, yana sane da dukan abin da suke yi.

16. Ba saboda ƙarfin mayaƙa sarki yakan ci nasara ba,Mayaƙi ba yakan yi rinjaye saboda ƙarfinsa ba.

17. Dawakan yaƙi ba su da amfani don cin nasara,Ƙarfin nan nasu ba zai iya ceto ba.