Littafi Mai Tsarki

Zab 33:20-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Ga Ubangiji muke sa zuciya,Shi mai taimakonmu ne, mai kiyaye mu.

21. Saboda da shi muke murna,Muna dogara ga sunansa mai tsarki.

22. Ka sa madawwamiyar ƙaunarka ta kasance tare da mu, ya Ubangiji,Da yake a gare ka muke sa zuciya.