Littafi Mai Tsarki

Zab 31:19-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Abin al'ajabi ne irin tanadin da ka yi wa masu tsoronka!Abin da kake aikatawa a gaban kowa kuma,Yana da banmamaki.Kana kiyaye waɗanda suke amincewa da kai.

20. Ka ɓoye su a wurinka lafiya daga makircin mutane,A inuwa mai lafiya ka ɓoye su daga zargin magabtansu.

21. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!Gama ya nuna mini ƙaunarsa mai ban al'ajabi,Sa'ad da aka kewaye ni, aka fāɗa mini!

22. Na ji tsoro, na zaci ka jefar da ni ne daga gabanka.Amma ka ji kukana sa'ad da na yi kira gare ka neman taimako.

23. Ku ƙaunaci Ubangiji, ku amintattun jama'arsa duka!Ubangiji yana kiyaye masu aminci,Amma yakan hukunta masu girmankai da tsanani.

24. Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali,Dukanku da kuke sa zuciya ga Ubangiji!