Littafi Mai Tsarki

Zab 3:4-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Na yi kira wurin Ubangiji domin taimako,Ya kuwa amsa mini daga tsattsarkan dutsensa.

5. Na kwanta na yi barci,Na kuwa tashi lafiya lau,Gama Ubangiji yana kiyaye ni.

6. Ba na jin tsoron dubban abokan gābaWaɗanda suka kewaye ni ta kowane gefe.

7. Ka zo, ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna!Ka yi nasara a kan dukan abokan gābana,Ka hallakar da dukan mugaye.

8. Ceto yana zuwa daga wurin Ubangiji,Bari yă sa wa jama'arsa albarka!