Littafi Mai Tsarki

Zab 29:5-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Muryar Ubangiji takan karya itatuwan al'ul,Har ma da itatuwan al'ul na Lebanon.

6. Yakan sa duwatsun Lebanon su yi tsalle kamar 'yan maruƙa,Ya kuma sa Dutsen Harmon ya yi tsalle kamar ɗan maraƙi.

7. Muryar Ubangiji ta sa walƙiya ta walƙata.

8. Muryarsa ta sa hamada ta girgiza,Ta girgiza hamadar Kadesh.

9. Muryar Ubangiji ta sa barewa ta haihu,Ta sa itatuwa su kakkaɓe,Sa'ad da aka yi sowa a cikin Haikalinsa,Aka ce, “Daukaka ga Allah!”

10. Ubangiji yana sarautar ruwa mai zurfi,Yana sarauta kamar sarki har abada.

11. Ubangiji yana ba jama'arsa ƙarfi,Ya sa musu albarka da salama.