Littafi Mai Tsarki

Zab 29:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku yabi Ubangiji, ku alloli,Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa.

2. Ku yabi sunan Ubangiji mai daraja,Ku rusuna a gaban Mai Tsarki sa'ad da ya bayyana.

3. An ji muryar Ubangiji a kan tekuna,Allah Maɗaukaki ya yi tsawa,Tsawar muryarsa kuwa ta yi amsa kuwa a bisa teku.