Littafi Mai Tsarki

Zab 26:4-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ba na tarayya da mutanen banza,Ba abin da ya gama ni da masu riya.

5. Ina ƙin tarayya da masu mugunta,Nakan kauce wa mugaye.

6. Ya Ubangiji, na wanke hannuwanaDon in nuna ba ni da laifi,Da ibada nakan taka, ina kewaya bagadenka.

7. Na raira waƙar godiya,Na faɗi dukan ayyukanka masu banmamaki.