Littafi Mai Tsarki

Zab 24:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Duniya da dukan abin da yake cikinta na Ubangiji ne,Duniya da dukan mazaunanta nasa ne.

2. Ya gina ta a bisa ruwa mai zurfi na ƙarƙashin ƙasa,Ya kuma kafa harsashinta a zurfin teku.

3. Wa yake da iko yă hau tudun Ubangiji?Wa yake da iko ya shiga Haikalinsa tsattsarka?

4. Sai wanda yake da tsarki cikin aiki, da tunani,Wanda ba ya yi wa gumaka sujada,Ko kuma yă yi alkawarin ƙarya.

5. Ubangiji zai sa masa albarka,Allah Mai Cetonsa zai kuɓutar da shi.

6. Su ne irin mutanen da suke zuwa wurin Allah,Waɗanda suke zuwa a gaban Allah na Yakubu.

7. A buɗe ƙofofi sosai,A buɗe daɗaɗɗun ƙofofi,Babban Sarki kuwa zai shigo!

8. Wane ne wannan babban Sarki?Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko,Ubangiji mai nasara cikin yaƙi!

9. A buɗe ƙofofi sosai,A buɗe daɗaɗɗun ƙofofi,Babban Sarki kuwa zai shigo!

10. Wane ne wannan babban Sarki?Ubangiji Mai Runduna, shi ne babban Sarki!