Littafi Mai Tsarki

Zab 22:8-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Suka ce, “Ka dogara ga Ubangiji,Me ya sa bai cece ka ba?Idan Ubangiji na sonka,Don me bai taimake ka ba?”

9. Kai ne ka fito da ni lafiya a lokacin da aka haife ni,A lokacin da nake jariri ka kiyaye ni.

10. Tun daga lokacin da aka haife ni nake dogara gare ka,Kai ne Allahna tun daga ran da aka haife ni.

11. Kada ka yi nisa da ni!Wahala ta gabato,Ba kuwa mai taimako.

12. Magabta da yawa sun kewaye ni kamar bijimai,Dukansu suna kewaye da ni,Kamar bijimai masu faɗa na ƙasar Bashan.

13. Sun buɗe bakinsu kamar zakoki,Suna ruri, suna ta bina a guje.

14. Ƙarfina ya ƙare,Ya rabu da ni kamar ruwan da ya zube ƙasa.Dukan gaɓoɓina sun guggulle,Zuciyata ta narke kamar narkakken kakin zuma.

15. Maƙogwarona ya bushe kamar ƙura,Harshena kuma na liƙe wa dasashina na sama.Ka bar ni matacce cikin ƙura.

16. Ƙungiyar mugaye na kewaye da ni,Suka taso mini kamar garken karnuka,Suka soke hannuwana da ƙafafuna.

17. Ana iya ganin ƙasusuwana duka.Magabtana suka dube ni, suka zura mini ido.

18. Suka rarraba tufafina a tsakaninsu,Suka jefa kuri'a a kan babbar rigata.

19. Kada ka yi nisa da ni, ya Ubangiji!Ka gaggauta ka cece ni, ya Mai Cetona!

20. Ka cece ni daga takobi,Ka ceci raina daga waɗannan karnuka.