Littafi Mai Tsarki

Zab 22:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Allahna, ya Allahna,Don me ka yashe ni?Na yi kuka mai tsanani, ina neman taimako,Amma har yanzu ba ka zo ba!

2. Da rana na yi kira a gare ka, ya Allahna,Amma ba ka amsa ba.Da dare kuma na yi kira,Duk da haka ban sami hutawa ba.

3. Amma an naɗa ka Mai Tsarki,Wanda Isra'ila suke yabonsa.

4. Kakanninmu suka dogara gare ka,Sun dogara gare ka, ka kuwa cece su.

5. Suka yi kira gare ka, suka tsira daga hatsari,Suka dogara gare ka, ba su kuwa kunyata ba.

6. A yanzu dai ni ba mutum ba ne, tsutsa ne kawai,Rainanne, abin ba'a ga kowa da kowa!

7. Duk wanda ya gan niSai yă maishe ni abin dariya,Suna zunɗena da harshensu suna kaɗa kai.

8. Suka ce, “Ka dogara ga Ubangiji,Me ya sa bai cece ka ba?Idan Ubangiji na sonka,Don me bai taimake ka ba?”

9. Kai ne ka fito da ni lafiya a lokacin da aka haife ni,A lokacin da nake jariri ka kiyaye ni.

10. Tun daga lokacin da aka haife ni nake dogara gare ka,Kai ne Allahna tun daga ran da aka haife ni.