Littafi Mai Tsarki

Zab 2:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Don me al'ummai suke shirin tayarwa?Don me waɗannan mutane suke ƙulla shawarwarin banza?

2. Sarakunan duniya sun yi tayarwa,Masu mulkinsu suna shirya maƙarƙashiya tare,Gāba da Ubangiji da zaɓaɓɓen sarkinsa.

3. Suna cewa, “Bari mu 'yantar da kanmu daga mulkinsu,Bari mu fice daga ƙarƙashinsu!”