Littafi Mai Tsarki

Zab 18:47-50 Littafi Mai Tsarki (HAU)

47. Yakan ba ni nasara a kan magabtana,Yakan sa jama'a a ƙarƙashina,

48. Yakan cece ni daga maƙiyana.Ka ba ni nasara a kan magabtana, ya Ubangiji,Ka kiyaye ni daga mutane masu kama-karya,

49. Don haka zan yabe ka a cikin al'ummai,Zan raira maka yabo.

50. Kullayaumi Allah yakan ba sarkin da ya naɗa babbar nasara.Yakan nuna madawwamiyar ƙauna ga wanda ya zaɓa,Wato Dawuda da zuriyarsa har abada.