Littafi Mai Tsarki

Zab 18:37-49 Littafi Mai Tsarki (HAU)

37. Na kori magabtana, har na kama su,Ba zan tsaya ba, sai na yi nasara da su.

38. Zan buge su har ƙasa, ba kuwa za su tashi ba,Za su fāɗi ƙarƙashin ƙafafuna.

39. Kakan ba ni ƙarfin yin yaƙi,Kakan ba ni nasara a kan magabtana.

40. Ka kori magabtana daga gare ni,Zan hallaka waɗanda suke ƙina.

41. Suna kukan neman taimako, amma ba wanda zai iya cetonsu,Za su yi kira ga Ubangiji, amma ba zai amsa ba.

42. Zan murƙushe su har su zama ƙuraWadda iska take kwashewa,Zan tattake su kamar caɓi a titi.

43. Ka cece ni daga mutane masu tawaye,Ka naɗa ni in yi mulkin sauran al'umma,Jama'ar da ban san ta ba, ta zama abin mulkina.

44. Za su yi biyayya sa'ad da suka ji ni,Baƙi za su rusuna mini,

45. Za su karai,Su fita, suna rawar jiki daga kagaransu.

46. Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga mai kāre ni!Allah ne, Mai Cetona! A yi shelar girmansa!

47. Yakan ba ni nasara a kan magabtana,Yakan sa jama'a a ƙarƙashina,

48. Yakan cece ni daga maƙiyana.Ka ba ni nasara a kan magabtana, ya Ubangiji,Ka kiyaye ni daga mutane masu kama-karya,

49. Don haka zan yabe ka a cikin al'ummai,Zan raira maka yabo.