Littafi Mai Tsarki

Zab 18:31-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. Ubangiji shi kaɗai ne Allah,Allah ne kaɗai kāriyamu.

32. Shi ne Allahn da yake ƙarfafa ni,Yana kiyaye lafiyata a kan hanya.

33. Yana sa in tabbata lafiya nake tafiya, kamar barewa.Yana kiyaye ni lafiya a kan duwatsu.

34. Yakan horar da ni don yaƙi,Domin in iya amfani da baka mafi ƙarfi.

35. Ya Ubangiji ka kiyaye ni, ka cece ni,Na zama babban mutum saboda kana lura da ni,Ikonka kuma ya kiyaye lafiyata.

36. Ka tsare ni, ba a kama ni ba,Ban kuwa taɓa fāɗuwa ba.