Littafi Mai Tsarki

Zab 16:9-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Don haka cike nake da murna da farin ciki,Kullum kuwa ina jin kome lafiya yake,

10. Saboda ba za ka yarda in shiga lahira ba,Ba za ka bar wanda kake ƙauna a zurfafa daga ƙarƙas ba.

11. Za ka nuna mini hanyar rai,Kasancewarka takan sa in cika da farin ciki,Taimakonka kuwa yana kawo jin daɗi har abada.