Littafi Mai Tsarki

Zab 149:6-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Bari su yi sowa da ƙarfiSa'ad da suke yabon Allah, da takubansu masu kaifi.

7. Don su ci nasara bisa al'ummai,Su kuma hukunta wa jama'a,

8. Su ɗaure sarakunansu da sarƙoƙi,Su ɗaure shugabanninsu da sarƙoƙin baƙin ƙarfe,

9. Su hukunta wa al'ummai, kamar yadda Allah ya umarta.Wannan shi ne cin nasarar jama'ar Allah!Yabo ya tabbata ga Ubangiji!