Littafi Mai Tsarki

Zab 147:3-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Yakan warkar da masu karyayyiyar zuciya,Yakan ɗaure raunukansu.

4. Ya ƙididdige yawan taurari,Yakan kira kowanne da sunansa.

5. Ubangijinmu mai girma ne, Mai Iko Dukka,Saninsa ya fi gaban aunawa.

6. Yakan ɗaukaka masu tawali'u,Amma yakan ragargaza mugaye har ƙasa.

7. Ku raira waƙar yabo ga Ubangiji,Ku yabi Allah da garaya.

8. Ya shimfiɗa gajimare a sararin al'arshi.Ya tanada wa duniya ruwan sama,Ya sa ciyayi su tsiro a kan tuddai.

9. Yakan ba dabbobi abincinsu,Yakan ciyar da 'ya'yan hankaki sa'ad da suka yi kuka gare shi.

10. Ba ya jin daɗin ƙarfafan dawakai,Ba ya murna da jarumawan mayaƙa.

11. Amma yana jin daɗin waɗanda suke tsoronsa,Yana jin daɗin waɗanda suke dogara da madawwamiyar ƙaunarsa.

12. Ya Urushalima, ki yabi Ubangiji,Ya Sihiyona, ki yabi Allahnki.

13. Shi yake riƙe da ƙofofinki da ƙarfi,Yakan sa wa jama'arki albarka.

14. Yakan kiyaye kan iyakar ƙasarki lafiya,Yakan kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau.

15. Yakan ba da umarni,Nan da nan umarnin yakan iso duniya.

16. Yakan aiko da dusar ƙanƙara mai kauri kamar ulu,Ya watsa jaura kamar ƙura.