Littafi Mai Tsarki

Zab 144:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, mai kiyaye ni,Ya hore ni don yaƙi,Ya kuwa shirya ni don yaƙi.

2. Shi yake kiyaye ni,Shi yake kāre ni,Shi ne mafakata da Mai Cetona,Wanda nake dogara gare shiDon samun zaman lafiya.Shi ne ya ɗora ni a kan al'ummai.

3. Ya Ubangiji wane ne mutum, har da kake lura da shi?Wane ne ɗan adam kurum, har da kake kulawa da shi?

4. Shi kamar hucin iska yake,Kwanakinsa kuwa kamar inuwa mai wucewa ne.

5. Ya Ubangiji, ka kware sararin sama, ka sauko,Ka taɓa duwatsu, don su tuƙaƙo da hayaƙi.

6. Ka aiko da walƙiyar tsawa ta warwatsa maƙiyanka,Ka harba kibanka, ka sa su sheƙa a guje!

7. Ka sunkuyo daga Sama,Ka tsamo ni daga cikin ruwa mai zurfi, ka cece ni,Ka cece ni daga ikon baƙi,

8. Waɗanda ba su taɓa faɗar gaskiya ba,Sukan yi rantsuwar ƙarya.