Littafi Mai Tsarki

Zab 143:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Ubangiji ka ji addu'ata,Ka kasa kunne ga roƙona!Kai adali ne mai aminci,Don haka ka amsa mini!

2. Ni bawanka, kada ka gabatar da ni a gaban shari'a,Gama ba wanda ba shi da laifi a gare ka.

3. Maƙiyina ya tsananta mini,Ya kore ni fata-fata.Ya sa ni a kurkuku mai duhu,Ina kama da waɗanda suka daɗe da mutuwa,

4. Don haka ina niyya in fid da zuciya,Ina cikin damuwa mai zurfi.