Littafi Mai Tsarki

Zab 139:6-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Yadda ka san ni ya fi ƙarfin magana,Ya yi mini zurfi, ya fi ƙarfin ganewata.

7. Ina zan tafi in tsere wa Ruhunka?Ina zan gudu in tsere maka?

8. Idan na hau cikin samaniya kana can,In na kwanta a lahira kana can,

9. In na tashi sama, na tafi, na wuce gabas,Ko kuma na zauna a can yamma da nisa,

10. Kana can domin ka bi da ni,Kana can domin ka taimake ni.

11. Da na iya roƙon duhu ya ɓoye ni,Ko haske da yake kewaye da niYa zama dare,

12. Amma har duhun ma, ba duhu ba ne a gare ka,Dare kuwa haskensa kamar na rana ne.Duhu da haske, duk ɗaya ne gare ka.

13. Kai ne ka halicci kowace gaɓa ta jikina,Kai ne ka harhaɗa ni a cikin mahaifiyata.

14. Ina yabonka gama kai abin tsoro ne,Dukan abin da ka yi sabo ne, mai banmamaki.Da zuciya ɗaya na san haka ne.