Littafi Mai Tsarki

Zab 137:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A bakin kogunan BabilaMuka zauna muka yi ta kuka,Sa'ad da muka tuna da Sihiyona.

2. A rassan itatuwan wardi da suke kusa da muMuka rataye garayunmu.

3. Waɗanda suka kama mu suka sa mu mu yi waƙa,Suka ce mana, “Ku yi mana shagaliDa waƙar da aka raira wa Sihiyona!”