Littafi Mai Tsarki

Zab 136:15-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Shi ne ya sa ruwa ya ci Fir'auna da rundunarsa,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

16. Ya bi da jama'arsa cikin hamada,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

17. Ya karkashe sarakuna masu iko,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

18. Ya karkashe shahararrun sarakuna,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

19. Ya kashe Sihon, Sarkin Amoriyawa,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

20. Ya kashe Og, Sarkin Bashan,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

21. Ya ba da ƙasarsu ga jama'arsa,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

22. Ya ba da ita ga bawansa Isra'ila,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

23. Bai manta da mu sa'ad da aka yi nasara da mu ba,Gama ƙaunarsa madawwamiyar ce.

24. Ya 'yantar da mu daga abokan gābanmu,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.