Littafi Mai Tsarki

Zab 136:11-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Shi ya fito da jama'ar Isra'ila daga cikin Masar,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

12. Da ƙarfinsa da ikonsa ya fito da su,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

13. Shi ne ya keta Bahar Maliya biyu,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

14. Shi ya bi da jama'arsa ta cikin tekun,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

15. Shi ne ya sa ruwa ya ci Fir'auna da rundunarsa,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

16. Ya bi da jama'arsa cikin hamada,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

17. Ya karkashe sarakuna masu iko,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

18. Ya karkashe shahararrun sarakuna,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

19. Ya kashe Sihon, Sarkin Amoriyawa,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

20. Ya kashe Og, Sarkin Bashan,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

21. Ya ba da ƙasarsu ga jama'arsa,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

22. Ya ba da ita ga bawansa Isra'ila,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.