Littafi Mai Tsarki

Zab 135:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku yabi Ubangiji!Ku yabi sunansa, ku bayin Ubangiji,

2. Ku da kuke tsaye a Haikalin Ubangiji,A wuri mai tsarki na Allahnmu.

3. Ku yabi Ubangiji, domin nagari ne shi,Ku raira yabbai ga sunansa, domin shi mai alheri ne.

4. Ya zaɓar wa kansa Yakubu,Jama'ar Isra'ila kuwa tasa ce.

5. Na sani Ubangijinmu mai girma ne,Ya fi dukan alloli girma.

6. Yana aikata dukan abin da ya ga dama a Sama ko a duniya,A tekuna, da kuma zurfafan da suke ƙarƙas.

7. Yakan kawo gizagizan hadiri daga bangayen duniya,Yakan yi walƙiya domin hadura,Yakan fito da iska daga cikin taskarsa.

8. A Masar ne ya karkashe 'ya'yan fari na mutane da na dabbobi.

9. A can ne ya aikata mu'ujizai da al'ajabai,Domin ya hukunta Fir'auna da dukan hukumar ƙasarsa.

10. Ya hallakar da sauran al'umma masu yawa,Ya karkashe sarakuna masu iko, wato

11. Sihon, Sarkin Amoriyawa, da Og, Sarkin Bashan,Da dukan sarakunan Kan'ana.

12. Ya ba da ƙasarsu ga jama'arsa,Ya ba da ita ga Isra'ila.

13. Ya Ubangiji, kullayaumi mutane za su sani kai ne Allah,Dukan tsararraki za su tuna da kai.

14. Ubangiji zai ji juyayin mutanensa,Zai 'yantar da bayinsa.