Littafi Mai Tsarki

Zab 129:3-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Suka sa mini raunuka masu zurfi a bayana,Suka mai da shi kamar gonar da aka nome.

4. Amma Ubangiji mai adalci,Ya 'yantar da ni daga bauta.”

5. Allah ya sa duk waɗanda suke ƙin Sihiyona,A yi nasara da su a kuma kore su!

6. Allah ya sa su zama kamar ciyawar da take girma a kan soraye,Ta kuwa bushe kafin ta isa yanka.

7. Ba wanda zai tattara ta,Ya ɗaure ta dami dami.