Littafi Mai Tsarki

Zab 126:4-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ya Ubangiji, ka komar da mu ƙasarmuKamar yadda ruwan da kake yi yakan koma cikin busassun koguna,

5. Ka sa waɗanda suke kuka a lokacin da suke dashe,Su tattara albarkar kaka da farin ciki!

6. Su waɗanda suka yi kuka a sa'ad da suka fita suna ɗauke da iri,Za su komo ɗauke da albarkar kaka,Suna raira waƙa don farin ciki!