Littafi Mai Tsarki

Zab 126:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da Ubangiji ya komar da mu cikin Sihiyona,Sai abin ya zama kamar mafarki!

2. Muka kece da dariya, muka raira waƙa don farin ciki,Sa'an nan sai sauran al'umma suka ambace mu, suka ce,“Ubangiji ya yi manyan al'amura masu girma, sabili da su!”

3. Hakika ya aikata manyan al'amura sabili da mu,Mun kuwa yi farin ciki ƙwarai!