Littafi Mai Tsarki

Zab 124:3-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Da sun haɗiye mu da rai a lokacin nan,Saboda zafin fushi da suke yi da mu,

4. Da rigyawa ta kwashe mu,Da ruwa yi ci mu,

5. Kwararowar ruwa ya nutsar da mu.”

6. Sai mu gode wa Ubangiji,Da bai bar abokan gābanmu su hallaka mu ba.

7. Mun kuɓuta kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta,Tarkon ya tsinke, mun 'yantu!

8. Taimakonmu daga wurin Ubangiji yake zuwa,Shi wanda ya yi sama da duniya.