Littafi Mai Tsarki

Zab 124:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da a ce Ubangiji ba ya tare da mu,Da me zai faru?Ba da amsa, ya Isra'ila!

2. “Da a ce Ubangiji ba ya tare da mu,A lokacin da abokan gābanmu suka auka mana,

3. Da sun haɗiye mu da rai a lokacin nan,Saboda zafin fushi da suke yi da mu,

4. Da rigyawa ta kwashe mu,Da ruwa yi ci mu,

5. Kwararowar ruwa ya nutsar da mu.”