1. Na yi murna sa'ad da suka ce mini,“Tashi mu tafi Haikalin Ubangiji!”
2. Ga shi kuwa, mun iso,Muna tsaye a ƙofofin Urushalima!
3. Urushalima birni ce wadda aka maido ta yadda take dā,Da kyakkyawan tsari, a shirye!
4. A nan kabilai sukan zo,Kabilan Isra'ila,Domin su yi godiya ga Ubangiji,Kamar yadda ya umarce su.
5. A nan majalisu suke,Wurin da sarki yake yi wa jama'arsa shari'a.
6. Ku yi wa Urushalima addu'ar salama!“Allah ya sa masu ƙaunarki su arzuta!
7. Salama ta samu a garukanki,Da zaman lafiya kuma a fādodinki.”
8. Saboda abokaina da aminaina,Na ce wa Urushalima, “Salama a gare ki!”
9. Saboda Haikalin Ubangiji, Allahnmu,Ina addu'a domin ki arzuta.