Littafi Mai Tsarki

Zab 120:4-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Da kibau masu tsini na mayaƙa,Da garwashin wuta zai hukunta ku!

5. Zama tare da ku mugun abu ne, kamar zama a Meshek,Ko tare da mutanen Kedar!

6. Na daɗe ƙwarai ina zama tare da mutane marasa son salama!

7. Sa'ad da nake maganar salama,Su sai su yi ta yaƙi.