Littafi Mai Tsarki

Zab 120:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da nake shan wahala,Na yi kira ga Ubangiji,Ya kuwa amsa mini.

2. Ka cece ni, ya Ubangiji,Daga maƙaryata da masu ruɗi!

3. Ku maƙaryata, me Allah zai yi da ku?Yaya zai hukunta ku?

4. Da kibau masu tsini na mayaƙa,Da garwashin wuta zai hukunta ku!

5. Zama tare da ku mugun abu ne, kamar zama a Meshek,Ko tare da mutanen Kedar!

6. Na daɗe ƙwarai ina zama tare da mutane marasa son salama!

7. Sa'ad da nake maganar salama,Su sai su yi ta yaƙi.