Littafi Mai Tsarki

Zab 119:83-89 Littafi Mai Tsarki (HAU)

83. Na zama marar amfani kamar salkar ruwan inabi wanda aka jefar da ita,Duk da haka ban manta da umarnanka ba.

84. Har yaushe zan yi ta jira?Yaushe za ka yi wa waɗanda suke tsananta mini hukunci?

85. Masu girmankai, waɗanda ba su biyayya da dokarka,Sun haƙa wushefe don su kama ni.

86. Umarnanka duka, abin dogara ne,Mutane suna tsananta mini da ƙarairayi,Ka taimake ni!

87. Sun kusa ci wa burinsu na su kashe ni,Amma ban raina ka'idodinka ba.

88. Saboda madawwamiyar ƙaunarka, ka yi mini alheri,Domin in yi biyayya da dokokinka.

89. Maganarka tabbatacciya ce, ya Ubangiji,A kafe take a Sama.