Littafi Mai Tsarki

Zab 119:155-157 Littafi Mai Tsarki (HAU)

155. Ba za a ceci mugaye ba,Saboda ba su yi biyayya da dokokinka ba.

156. Amma juyayinka yana da girma, ya Ubangiji,Saboda haka ka cece ni yadda ka yi niyya.

157. Maƙiyana da masu zaluntata, suna da yawa,Amma ban fasa yin biyayya da dokokinka ba.