Littafi Mai Tsarki

Zab 119:15-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Nakan yi nazarin umarnanka,Nakan kuma yi bimbinin koyarwarka.

16. Ina murna da dokokinka,Ba zan manta da umarnanka ba.

17. Ka yi mini alheri, ni bawanka,Domin in rayu in yi biyayya da koyarwarka.

18. Ka buɗe idonaDomin in ga gaskiyar shari'arka mai banmamaki.

19. Zamana a nan duniya na ɗan lokaci kaɗan ne.Kada ka ɓoye mini umarnanka!

20. Zuciyata ta ƙosa saboda marmari,A kowane lokaci ina so in san hukuntanka.