Littafi Mai Tsarki

Zab 119:142-160 Littafi Mai Tsarki (HAU)

142. Adalcinka zai tabbata har abada,Dokarka gaskiya ce koyaushe.

143. A cike nake da wahala da damuwa,Amma umarnanka suna faranta zuciyata.

144. Koyarwarka masu adalci ne har abada,Ka ba ni ganewa domin in rayu.

145. Ina kira gare ka da zuciya ɗaya,Ka amsa mini, ya Ubangiji,Zan yi biyayya da umarnanka!

146. Ina kira gare ka,Ka cece ni, zan bi ka'idodinka!

147. Tun kafin fitowar rana ina kira gare ka neman taimako,Na sa zuciya ga alkawarinka.

148. Dare farai ban yi barci ba,Ina ta bimbini a kan koyarwarka.

149. Ka ji ni, ya Ubangiji, bisa ga madawwamiyar ƙaunarka,Ka kiyaye raina bisa ga alherinka!

150. Mugayen nan waɗanda suke tsananta mini sun matso kusa,Mutanen da ba su taɓa kiyaye dokarka ba.

151. Amma kana kusa da ni, ya Ubangiji,Dukan alkawaranka gaskiya ne.

152. Tuntuni na ji labarin koyarwarka,Ka sa su tabbata har abada.

153. Ka dubi wahalata, ka cece ni,Gama ban ƙi kulawa da dokarka ba.

154. Ka kāre manufata, ka kuɓutar da ni,Ka cece ni kamar yadda ka alkawarta!

155. Ba za a ceci mugaye ba,Saboda ba su yi biyayya da dokokinka ba.

156. Amma juyayinka yana da girma, ya Ubangiji,Saboda haka ka cece ni yadda ka yi niyya.

157. Maƙiyana da masu zaluntata, suna da yawa,Amma ban fasa yin biyayya da dokokinka ba.

158. Sa'ad da na dubi waɗannan maciya amana,Sai in ji ƙyama ƙwarai,Domin ba su yi biyayya da umarninka ba.

159. Ka dubi yadda nake ƙaunar koyarwarka, ya Ubangiji!Ka cece ni bisa ga madawwamiyar ƙaunarka.

160. Cibiyar dokarka gaskiya ce,Dukan ka'idodinka na adalci tabbatattu ne.