Littafi Mai Tsarki

Zab 118:16-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Ikonsa ne ya kawo mana nasara,Babban ikonsa a wurin yaƙi!”

17. Ba zan mutu ba, amma rayuwa zan yi,Don in ba da labarin abin da Ubangiji ya yi.

18. Ya hukunta ni da hukunci mai tsanani,Amma bai kashe ni ba.

19. A buɗe mini ƙofofin Haikali,Zan shiga ciki in yabi Ubangiji!

20. Wannan ƙofar Ubangiji ce,Sai adalai kaɗai suke shiga ciki!

21. Ina yabonka, ya Ubangiji, domin ka ji ni,Domin ka ba ni nasara!

22. Dutsen da magina suka ƙi, wai ba shi da amfani,Sai ya zama shi ya fi duka amfani.

23. Ubangiji ne ya yi haka,Wannan kuwa abin banmamaki ne!

24. Wace irin rana ce haka da Ubangiji ya ba mu!Bari mu yi farin ciki, mu yi biki!

25. Ka cece mu, ya Ubangiji, ka cece mu!Ka ba mu nasara, ya Ubangiji!

26. Allah yakan sa wa wanda ya zo da sunan Ubangiji albarka!Daga Haikalin Ubangiji muke yabonka!

27. Ubangiji shi ne Allah, yana yi mana alheri,Ku ɗauki hadayunku ku yi ta idi,Ku ɗaura su a zankayen bagade.