Littafi Mai Tsarki

Zab 118:16-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Ikonsa ne ya kawo mana nasara,Babban ikonsa a wurin yaƙi!”

17. Ba zan mutu ba, amma rayuwa zan yi,Don in ba da labarin abin da Ubangiji ya yi.

18. Ya hukunta ni da hukunci mai tsanani,Amma bai kashe ni ba.

19. A buɗe mini ƙofofin Haikali,Zan shiga ciki in yabi Ubangiji!