Littafi Mai Tsarki

Zab 118:10-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ma ƙiya da yawa sun kewaye ni,Amma na hallaka su ta wurin ikon Ubangiji!

11. Suka kewaye ni a kowane gefeAmma na hallaka su ta wurin ikon Ubangiji!

12. Suka rufe ni kamar ƙudan zuma,Amma suka ƙone nan da nan kamar wutar jeji,Ta wurin ikon Ubangiji na hallaka su!

13. Aka auko mini da tsanani,Har aka kore ni,Amma Ubangiji ya taimake ni.

14. Ubangiji yakan ba ni iko, ya ƙarfafa ni,Shi ne Mai Cetona!

15. Ku kasa kunne ga sowar murna ta nasaraA cikin alfarwan jama'ar Allah.“Ikon Ubangiji mai girma ne ya aikata wannan!

16. Ikonsa ne ya kawo mana nasara,Babban ikonsa a wurin yaƙi!”

17. Ba zan mutu ba, amma rayuwa zan yi,Don in ba da labarin abin da Ubangiji ya yi.

18. Ya hukunta ni da hukunci mai tsanani,Amma bai kashe ni ba.

19. A buɗe mini ƙofofin Haikali,Zan shiga ciki in yabi Ubangiji!

20. Wannan ƙofar Ubangiji ce,Sai adalai kaɗai suke shiga ciki!

21. Ina yabonka, ya Ubangiji, domin ka ji ni,Domin ka ba ni nasara!

22. Dutsen da magina suka ƙi, wai ba shi da amfani,Sai ya zama shi ya fi duka amfani.